Sabon kwamishinan Ilimi na jihar kano Dr. Ali Haruna Makoda ya kama aiki a hukumance, inda ya yi alkawarin kara bullo da wasu shirye-shirye da nufin bunkasa fannin ilimi a jihar nan.
Da yake jawabi ga ma’aikata, ma’aikatar ilimin, Dr. Makoda ya amince da dimbin tsare-tsare da gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da su tare da bayyana aniyarsa ta ciyar da su gaba.
Makoda ya kuma jaddada bukatar yin aiki tukuru da jajircewa don ganin ma’aikatar ta samu ci gaba, tare da baiwa ma’aikatan tabbacin ci gaba da fadada shirye-shirye masu kyau da tsohon kwamishinan ma’aikatar ya bullo da su.
Da yake jawabin bankwana, Kwamishina mai barin gado Alhaji Umar Haruna Doguwa ya nuna jin dadinsa da samun damar yin aiki a ma’aikatar tare da bayyana wasu nasarorin da aka samu a zamaninsa, wanda suka hada da kara yawan kasafin kudin da ake warewa fannin ilimi, Inda aka ware 30% a cikin 100 a Shekarar 2024 da 31% a Shekarar 2025.
A bangare guda, sabon babban sakataren ma’aikatar ilimi, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, yayi addu’ar Allah ya baiwa kwamishinonin biyu ikon yi musu jagoranci a sabbin ayyukan da aka ba su.
Sabon kwamishinan ilimi na Kano ya kama aiki
from Daily Post Nigeria https://ift.tt/ysegmQN
via IFTTT