Bukukuwan karshen shekara: Yan sanda sun kama sama da mutum 100 da makamai

‘Yan sanda sun kama mutane 128 da ake zargi da mallakar mugayen makamai da satar motoci a fadin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.

ACP Adejobi, ya ce yayin da ake gab da shiga lokacin bukukuwan karshen shekara, ‘yan sanda sun kara zama masu lura da kwazo, suna kara kokarin tabbatar da tsaron lafiyar dukkan ‘yan Najeriya da mazauna kasar.

Ya ce hakan ya haifar da nasarori da dama na kai samame, kama bata-gari da kuma kwato makamai.

“A bisa umarnin Sufeto-Janar na ‘yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D., NPM, na samar da ingantattun matakan tsaro domin yaki da laifuka a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara, jami’an ‘yan sanda na rundunar Najeriya a jihohi daban-daban sun gudanar da sintiri da samame, inda suka samu nasarar fatattakar bata-gari, kame su da kuma kwato makamai masu hadari,” in ji shi.

Bukukuwan karshen shekara: Yan sanda sun kama sama da mutum 100 da makamai



from Daily Post Nigeria https://ift.tt/hg4U7B0
via IFTTT

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form